A safiyar yau, Alhamis, 13 ga watan Nuwamba, 2025, na samu damar halartar taron bita na kwana daya bisa gayyatar majalisar limaman masallatan Juma’a ta reshen Jahar Kano’ a karkashin jagorancin shugabanta, Sheikh Dr. Muhammad Nasir Adam Tare da tallafin kungiyar tallafawa musulunci ta NUSRET wanda aka gabatar a masallacin Shelkh Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata
Na gabatar da jawabi tare da kira ga manyan Limamanmu da Malamai masu daraja da su ƙara kaimi wajen ilmantar da al’ummar musulmi kan yadda zasu gudanar da ibadunsu, musamman a al’amuran da suka shafi tsarki, alwala, da kuma sallah wadan nan abubuwa ne masu matuƙar muhimmanci a cikin addininmu waɗanda ke ƙarfafa alaƙarmu da Allah (S.W.A)
Ina kara samun kwarin guiwa a duk lokacin da na samu kaina a tsakanin Malamai na addini, waɗanda nake ɗauka a matsayin malamai kuma Iyaye gareni, Na kuma yi kira a gare su da su ci gaba da Jan hankulan mutanen mu zuwa ga ibada da bautawa Allah da ɗa’a maimakon shiga rigingimu kan akidun dake da alaka da al’amuran addini wanda suka gabata shekaru aru aru
Na kara tabbatar wa Shugabancin majalisar Limaman ta Jihar Kano karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Nasir Adam cewa ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida za ta cigaba da shirya tarukan bita ga limamai kamar yadda aka fara. Manufar Irin wannan tattaunawa ita ce a ci gaba da sanar da malamai shirye shiryen gwamnati da manufofin gwamnatin jihar Kano duba da muhimmiyar rawar da malamai suke takawa tsakanin gwamnati da al’umma.
Majalisar Limamai da Ƙungiyar Tallafawa Musulunci ta Nusret, sun Karramani da lambar yabo tare da ba ni tarin littattafai na Addini da ƙungiyar ta wallafa, domin girmamawa bisa ga gudummawar da na bayar wajen wayar da kan jama’a da kuma tallafawa ci gaban addini.
Taron bitar, wanda ya tara manyan Limamai daga sassan Jihar Kano, ya zama wata dama ta musayar ilimi da haɗin kai, da kuma ƙarfafa gwiwa tsakanin shugabannin addini da gwamnati wajen cigaban al’ummar mu.
Muna addu’a ga ALLAH, Ya cigaba da hada kan malaman mu’ domin zame wa Al ‘Umma dun kulalliya, cike da farin ciki, da kuma yalwar arziki.



More Stories
One Kano Agenda Appoints Waiya as Grand Patron, Commends Governor Abba 2026 Budget
OPEN LETTER TO THE PRESIDENT AND COMMANDER IN CHIEF OF THE ARM FORCES OF THE FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA, PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU
PRESS STATEMENT